1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran da MDD a game da shirin makamashin Nukiliya.

February 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6j

A yau jakadun majalisar dinkin duniya suka isa kasar Iran bayan da Iran din ta yi alkawarin amsa wasu tambayoyi domin kawar da shakkun da majalisar dinkin duniyar ke da shi a game da aikin sarrafa sinadarin Uranium da Iran din da cigaba da aiwatarwa wanda ake dangantawa da yunkurin kasar na kera makamin atom.

Jakadun na majalisar dinkin duniya sun baiyana cewa Iran ta cigaba da aiwatar da aiki a wasu cibiyoyin ta na nukiliya lamarin dake kara nuna cewa kasar na kann bakan ta na barazanar kera makamin nukiliya. Wani jakadan kungiyar tarayyar turai wanda ya shi ma, ya isa kasar Iran din tare da jakadun majalisar dinkin duniya ya ce ko da yake Iran ta yi alkawarin wasu muhimman tambayoyi, baya tsammanin bayanan zasu gamsar sosai a game da shirin ta na makamashin nukiliya. Batun nukiliyar kasar din an dade ana takaddama a kan sa inda Amurka da kungiyar tarayyar turai ke baiyana cewa akwai alamu dake nuna Iran na shirin mallakar makamin kare dangi wanda ke da barazana ga dorewar zaman lafiya a duniya. Iran ta musanta wannan zargi da cewa shirin ta na makamshin nukiliya na lumana ne domin samar da haske wutar lantarki ga alúmar ta.