1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta shawarci kasashen Musulmi su rage dogaro

Salissou Boukari
January 16, 2018

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani ya yi kira ga dukannin kasashen Musulmi da su kasance masu hadin kai, tare da nesantar dogaro da taimakon kasashen waje.

https://p.dw.com/p/2qvf9
Hassan Rohani
Shugaban kasar Iran Hassan RohaniHoto: picture-alliance/Iranian Presidency Office

Rohani ya yi wannan kalami ne yayin bude babban zaman taron hadin gwiwar 'yan majalisar dokoki na kungiyar kula da hulda tsakanin kasashen Musulmi ta OIC a Teheran babban birnin kasar Iran. Shugaba Rohani ya ce rashin dogoro da kasashen ketare da kuma hadin kai a tsakanin kasashen na Musulmai ne kawai zai sa a kauce wa irin matsalolin da kasashen na Musulmi ke fuskanta wajen samun bunkasa.

Sai dai kuma ya kara da cewa, ba wai yana nufi su nesantar da kansu daga sauran kasashe bane, inda ya tabo batun yarjejeniyar nukiliyar kasar ta Iran da aka cimma a watan Yuli na 2015 wanda kuma shugaban Amirka ke ta baranar fitar da kasarsa daga yarjejeniyar.

Hukumomin kasar ta Iran dai na shan suka daga masu ra'ayin rikau na kasar kan yarjejeniyar nukiliyar da suka ce an yi ta ne kawai don amfanin kasashen yamma, alhali kuma Shugaba Rohani na ta kokarin janyo hankalin masu zuba jari na kasashen Turai da su zo domin zuba jari a kasarsa.