1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta shirya wa matakin EU

October 17, 2022

Iran ta yi alkawarin maida martani cikin gaggawa ga Tarayyar Turai, daidai lokacin da kungiyar ke shirin bayyana takunkumai kan ta saboda zanga-zanga da ake yi a kasar.

https://p.dw.com/p/4IHov
Wasu ministocin kasashen EU da ke taro a Luxembourg
Hoto: Virginia May/AP Photo/picture alliance

Gwamnatin kasar Iran ta yi alkawarin maida martani cikin gaggawa ga kungiyar Tarayyar Turai, daidai lokacin da kungiyar ta shirya bayyana wasu takunkumai kan ta saboda zanga-zanga da mata ke yi yau sama da wata guda.

Ministocin kasashen EU sun hadu a wannan Litinin, domin dora wa Iran din takunkumai sakamakon zanga-zangar da ta biyo bayan mutuwar wata matashiya Mahsa Amini a ranar 16 ga watan jiya, da jami'an tabbatar da da'a suka tsare da laifin bijire wa hijabi.

Matakan da kasashen na Tarayyar Turai suka tsara dauka dai sun hada da hana wasu jami'an Iran su 11 takardun izinin shiga kasashen; ciki har da manyan jami'an Hisbah.

Da ma dai kasashen Amirka da Birtaniya da Canada sun sanar da wasu takunkuman a kan Iran suna zargin ta da take hakki.

Sai dai Iran din ta ce Amirka da kawayenta ne ke tsara boren da ake yi a kasar.