1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi belin Haleh Asfandiari

August 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuDV

Hukumomin Iran sun yi belin Haleh Esfandiari, wata mallamar jami´a ,da su ka tsare kurkuku tun watan Mayu da ya gabata, a sakamakon zargin da su ka yi mata na leƙen asiri.

Lauyar Esfandiari, wato Sherin Ebadi, mai fafatakar kare haƙƙoƙin bani adama a Iran,ta bayyana labarin.

Saidai hukumomin Teheran sun buƙaci ta biya diyyar Euro dubu 240 a matsayin kuɗin fidda takaici.

Haleh Esfandari mai shekaru 68 a dunia,yar ƙasar Iran ce, wadda ke zaune a Amurika, ta kuma sami takardar aihuwar Amurika.

Tun watan Mayu da ya wuce jami´an tsaro su ka capke ta, a Iran, tare da wasu mutane 2, wanda har yazu ke tsare kurkuku.

Ƙasar Amurika ta bayyana gamuswa da belin wannan mata, saidai ta yi kira ga Iran, ta sallami sauran mutanen 2, da ta tsare, bisa zargin da ba shi da tushe.