1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta ja kunnen Saudiyya kan harinta aYemen

Yusuf BalaJune 9, 2015

Jakadan kasar ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Gholamali Khoshroo ya bayyana cewa ofishin jakadancin na Iran a birnin Sanaa ya girgiza yayin da wasu bangarori nasa suka lalace lokacin farmakin.

https://p.dw.com/p/1FeGE
Jemen Luftangriff auf Sanaa
Hoto: Reuters/M. al-Sayaghi

Kasar Iran ta fada wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa wasu hare-hare har sau biyu da kasar Saudiyya ke kaiwa a Yemen sun afka kusa da ofishin jakadancinta a Yemen, sannan ta yi gargadin cewa za ta dauki martani mai kaushi idan hakan ta ci gaba da faruwa.

Jakadan kasar ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Gholamali Khoshroo ya bayyana a wata wasika da ta fito a ranar Talatan nan cewa, ofishin jakadancin na Iran a birnin Sanaa ya girgiza yayin da wasu bangarori nasa suka lalace lokacin da aka kai wani farmaki a ranar 25 ga watan Mayu, hakan nan kuma aka kara samun irin wannan farmaki a ranar ashirin ga watan Afrilu.

Al'ummar wannan kasa dai ta Yemen na ci gaba da kokawa da halin da suka tsinci kansu na lugudan wutar musamman wannan lokaci da ake tunkarar azumin watan Ramadana, kamar yadda Muhammad Ali wani mazaunin birnin Sanaa ke cewa:

"Mutane da dama sun rasa ayyukansu, mutane sun tsinci kai a wasu wurare cikin halin kaka na ka yi, ina ganin lamura na yi mana wahala, kuma al'ummar Yemen zasu fiskanci babbar barazana sakamakon wannan fada da ake yi".

Tun dai a watan Maris ne kasar ta Saudiyya ke jagorantar lugudan wuta kan mayakan na Houthi 'Yan shi'a da ke samun goyon bayan kasar ta Iran