1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi watsi da zargin hari kan jiragen ruwa

Abdul-raheem Hassan
June 14, 2019

Ma'ikatar harkokin wajen Iran ta ce ba gaskiya ba ne tuhumar da Amirka ke mata na kai hari kan wasu tankokin mai a gabar ruwan Oman, inda ta ce Amirka na neman tsananta rikici ne kawai.

https://p.dw.com/p/3KOnL
Iran Außenminister Mohammad Javad Zarif
Hoto: eghtesadonline

Cikin wani sakon martani ta shafinta na twitter, ma'aikatar tsaron Iran ta danganta zargin da makircin siyasa a daidai lokacin da Firaministan Japan ke ziyarar sasanta rikin Amirka da Iran.

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya ce an samu tabbacin wasu hotunan bidiyo da ke nuna dakarun Iran na cire wasu na'urorin da ake zaton nakiyoyi ne da ba su fashe ba daga daya daga cikin jirgin.

Kasar Iran na cewa tana da alhakin tsaro a gabar tekun Oman. Sabon cece-kuce tsakanin Iran da Amirka na sake haifar da shakku kan yunkurin sasanta rikicin kasuwanci da ya yi tsanani tsakanin kasashen biyu.