1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran tana mutunta yarjejeniyar da ha haramta yaɗuwar makaman nukiliya

January 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuVW

Babban wakilin Iran a tattunawar da ake game da shirinta na nukiliya Ali Larijani ya ce ko da yake kasarsa ta kuduri aniyar yin amfani da fasahar nukiliya a hanyoyi na lumana amma yayi gargadin cewa matsayin ta ka iya canzawa idan aka tsokane ta. Bayan tattaunawa ta yi ni biyu da yayi a birnin Beijing Larijani ya fadawa wani taron manema labarai cewa kasar sa na adawa da mallakar makaman nukiliya kuma zasu yi amfani da fasahar nukiliya a hanyoyin zaman lafiya karkashin yarjejeniyar da ta haramta yaduwar makaman nukiliya, amma idan aka yi masu barazana to komai na iya canzawa. Kwamitin sulhun MDD ya haramtawa kasashen duniya sayarwa Iran duk wasu abubuwa da Iran din zata iya amfani da su a shirin ta na nukiliya. China wadda ke da ikon hawa kujerar naki, amma ta goyi da bayan wannan mataki duk da kyakkyawar huldar cinikaiya dake tsakanin ta da Iran.