1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraqi ta fara gudanar da bincike kan hoton bidiyon rataye Saddam

January 3, 2007
https://p.dw.com/p/BuVh

Gwamnatin Iraqi ta kaddamar da bincike akan wani bidiyo na wayar salula da ke dauke da yadda aka rataye tsohon shugaban kasar Saddam Hussein kuma aka watsa ta intanat. Mabiya darikar Sunni a kasar sun fusata game da bidiyon. Wani jami´i na kurkusa da FM Iraqi Nuri al-Maliki ya ce binciken zai gano wanda ya dauki bidiyon a asurce lokacin da aka zartas da hukuncin kisan kan Saddam. Al-Maliki ya kuma nuna takiacin sa game da halin da ake ciki a kasar. A wata hira da mujallar Wall Street ta Amirka ta yi da shi, dan siyasar na darikar Shi´a ya ce ba ya sha´awar neman yin tazarce kuma ya na fata ma ba zai kammala wa´adin mulkinsa na farko ba.