1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS ta dau alhakin harin Faransa

Usman Shehu UsmanJuly 16, 2016

Kwana biyu bayan harin da ya hallaka muta 84 a birnin Nice, yanzu an samu kungiyar da ta ce ita ce ta kitsa kai harin wanda wani matashi ya kai da wata tirela.

https://p.dw.com/p/1JQ5H
Frankreich Blumen nahe des Anschlagortes in Nizza
Hoto: Reuters/P. Rossignol

A wata sanarwa da Kungiyar IS ta fitar ta ce, mutumin da ya kai harin a birnin Nice, na Faransa, wanda ya tattaka mutane da tirela, daya ne daga cikin sojojin IS. Sanarwar da suka fitar ta kafar sadawarsu, ta kara da cewa, mutumin ya kai harin ne don amsa kiran da aka yi na kai farmaki kan duk yan kashen da ke cikin kawancen kasashen da ke yaki da IS.

Biyo bayan wannan hari, Shugaban kasar Faransa Francois Hollande, ya soke wasu ziyarce-ziyarce da ya shirya yi, bayan harin ta'addanci a birnin Nice. Dama an shirya Hollande zai ziyarce kasashen Ostiriya, Silovakiya, da jamhuriyar Cek, inda ya tsara tattaunawa da shugabannin kasashen kan batun da ya shafi ballewar kasar Birtaniya daga kungiyar EU. Bayan kuri'ar ba za ta da ta amince wa Birtaniya ta fice daga EU, shugaban kasar Fransa Francois Hollande da Angela Merkel ta kasar Jamus da Firimiyan Italiya Matteo Renzi, suka yi alkawarin bude sabon babi a Kungiyar EU, musamman kan tsaro da samar da aiyyukan yi.