1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS ta kai harin kunar bakin wake a Libiya

Abdul-raheem Hassan
August 31, 2017

Mayakan kungiyar IS dau alhakin wani harin kunar bakin wake da ya hallaka jami'an rundunar sojoji hudu da wasu jami'an 'yansanda a kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/2jAic
Flash-Galerie Tripolis Gaddafi Libyen Luftangriff NATO
Hoto: picture alliance/dpa

Harin dai ya faru ne a lokacin da wata mota makare da ababen fashewasuka tarwatse a wani shingen binciken jami'a tsaro a garin al-Nofalia da ke da ke zama tsohon mafakan kungiyar IS.

Hukumomin tsaron kasra sun ce harin ya ritsa wasu jami'an 'yan sanda biyu. Saidai rundunar sojojin kasar ta na alakanta harin da harin kwantar bauna da ke da niyar ganin bayan wasu manyan dakaru da ke yankin.

A tun bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Libiyan Muammar Gaddafi da tsinin bindiga a shekara ta 2011, kasar ta fada cikin rudanin kungiyoyi masu faftuka da makamai.