1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS ta kashe mutane 232 a Mosul na Iraki

October 28, 2016

Mayakan kungiyar IS sun aikata ta'asa a Mosul inda suka yi amfani da bindiga wajen harbe mutane 232 galibinsu tsaffin sojoji, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/2Rq6N
Symbolbild Rakka Kämpfer der IS
Hoto: picture-alliance/dpa

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar Kungiyar IS ta murkushe mutane akalla 232 a kusa da Mosul, a daidai lokacin da dakarun gwamnatin Iraki suka durfafi birnin da nufin kwatoshi daga hannu masu kaifin kishin addini. A lokacin da take bayani a birnin Geneva na Switzerland, kakakin hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Ravina Shamdasani ta nunar da cewar akasarin wadanda ta'asar ta shafa tsaffin sojoji ne, kuma kashe-kashen sun wakana a kwanaki biyun da suka gabata.

Kafofi masu tushe sun ruwaito cewar mayakan kungiyar IS suna tilasta wa mazauna garuruwan da ke kewayen Mosul tattara wuri guda domin yin amfani da su a matsayin garkuwa a yakin da suke yi da sojojin Iraki da ke samun goyon bayan Amirka. A cewar hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya dai, 'yan bindigan IS sun tilasta wa dubban mutane kaurace wa matsugunansu domin tsira da rayukansu.