1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS ta sace 'yan kasar waje a Libiya

Ahmed SalisuMarch 9, 2015

Ma'aikatar harkokin wajen Austriya ta ce 'yan kungiyar IS sun sace wasu 'yan kasashe waje a kalla su tara a wajen tonon danyen mai na al-Ghani da ke kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/1Enrv
Symbolbild Islamischer Staat
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Mai magana da yawun ma'aikatar ta ce 'yan IS din ba su illata mutanen da suka kame ba kuma sanda suka kame su din dukanninsu na cikin koshin lafiya.

Mutanen dai sun hada ne da 'yan kasar ta Austriya da Jamhuriyar Czech da Bangladesh da Philippines da kuma wani dan Afrika da ba a tantance ko dan wace kasa ba ne. Ya zuwa yanzu dai IS ba su ce komai ba game da sace mutanen.

A baya dai kungiyar ta sace 'yan kasashen ketare da dama inda ta hallaka kusan dukanninsu ta hanyar yi musu yankan rago kamar yanda su kan nuna a faifan bidiyon da suke fiddawa.