1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israela ta fada cikin rudani na siyasa

May 2, 2007
https://p.dw.com/p/BuMN

Faraministan Israela Ehud Olmert yayi watsi da kiraye kirayen da yan jam´iyyar sa ta Kadima keyi, na murabus daga mukamin sa.

Bukatar yin murabus din dai ta biyo bayan samun hannun faraministan ne dumu dumu da nuna rashin adalci, a lokacin yakin da kasar ta gwabza da kasar Libanon.

An gano haka ne kuwa a yayin da wani kwamiti da aka dorawa alhakin bincike kann yakin ya fiddo da rahotan sane, a ranar litinin din data gabata.

Ci gaba da kiraye kirayen murabus din Faraministan dai ya biyo bayan murabus din da ministar harkokin wajen kasar , wato Tzipi Livni tayi ne a jiya talata.

A kuri´ar neman jin ra´ayin jama´a da aka gudanar an gano cewa kashi 65 na mutanen kasar na bukatar faraministan yin murabus daga mukamin nasa.

Mutane dai a kalla dubu daya da dari uku da sittin ne suka rasa rayukan su daga bangarorin biyu, a lokacin yakin da Israelan ta gwabza da kasar ta Libanon.