1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra´ila ba zata mutunta tayin tsagaita wuta da ´yan takifen Falasdinawa ba

November 24, 2006
https://p.dw.com/p/BuaW
Isra´ila ta yi watsi da tayin tsagaita wuta da kungiyoyin sojin sa kai na Falasdinawa suka yi mata. Mai magana da yawun gwamnatin Isra´ila ta ce ba za´a amince da tayin domin ya tanadi dakatar da harba rokoki ne kadai daga Zirin Gaza zuwa cikin Isra´ila. Kakakin ta ce Isra´ila zata daina farmakin sojin kadai idan sojojin sa kan Falasdinawa suka ajiye makansu. Da farko kungiyoyin na Falasdinawa sun bukaci Isra´ila ta kawo karshen matakan sojin da take dauka a Zirin Gaza da Gabar yamacin kogin Jordan. Fatah da Jihadin Islami na daga cikin kungiyoyin Falasdinawa masu gwagwarmaya da suka yi wannan tayi. A kuma can arewacin Gaza sojojin Isra´ila sun harbe wani dan kungiyar Hamas da kuma wani yaro dan shekaru 10 har lahira.