1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta fara tsagaita wuta a Gaza

August 4, 2014

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna takaicin game da harin da Isra'ila ta kai kan wata makaranta a Zirin Gaza. Sai dai kuma Isra'ila ta fara amfani da shirin tsagaita wuta.

https://p.dw.com/p/1CoIC
Hoto: picture-alliance/dpa

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya ce abin takaici ne harin da Isra'ila ta kai kan wata makaranta jiya Lahadi a Rafah da ke yankin Zirin Gaza na Falasdinu, wanda ya ce ya saba dokokin kasa da kasa. Kimanin 'yan gudun hijira 3000 suka tsere zuwa makarantar ta Majalisar Dinkin Duniya wadda ta fuskanci hari, kuma kimanin mutane 10 suka hallaka yayin da wasu suka samu raunika.

A wani labarin Isra'ila ta fara aiki da wani shirin tsagaita wuta na tsawon sa'oi bakwai daga safiyar wannan Litinin. Isra'ila ta ce shirin tsagaita wutar zai shafi dauki yankin Zirin Gaza, amma ban da gabashi Rafah, kuma ta yi haka ne bisa dalilan jinkai. Fiye da Falasdinawa 1800 suka hallaka samakaon rikicin, yayin da Isra'ila ta fara mutane fiye da 60.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe