1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai hare-hare a Zirin Gaza

Eleonore UhlichAugust 4, 2014

Dakarun ƙasar sun kashe wata yarinyar ƙarama 'yar kimanin shekaru takwas tare da jikkata wasu mutane 30, duk da yarjejeniyar tsaigata buɗe wuta da aka cimma.

https://p.dw.com/p/1Coaf
Nahostkonflikt Israel Rückzug aus dem Gazastreifen 3.8.2014
Hoto: Reuters/Nir Elias

An kai harin ne da makamai masu linzami da jiragen sama na yaƙi a kan wata cibiya ta 'yan gudun hijira da ke a yammancin Gaza a Chati. Wannan mutumin wani mazaunin unguwar ce ta Chati.

''Sun kashe iyalai da dama ,wani wurin dukkanini yalen gidan, an kashesu wannan rashin hankali ne, kuma ba za mu amince da shi ba.''

Ƙungiyar Hamas da Isra'ilan na zargin junansu da karya yarjeniyar. Tun farko gwamnatin Isra'ilan ta ce yarjejeniyar ba ta shafi yankin kudanci ba na Rafa.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe