1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israila ta saki mataimakin Firaministan Palasdinawa

September 27, 2006
https://p.dw.com/p/BuiB

Wata kotu a Israila a yau ta sako mataimakin Firaministan Palasdinwa Nasser Shaer,babban jamiin Hamas na farko ke nan da ta sake bayan tsare membobin Hamas da tayi.

Sai dai lauyansa yace kotun ta haramta masa zuwa ofishinsa dake birnin Ramallah na wucin gadi.

A ranar 19 ga watan Agusta ne jamian tsaronn Israila suka tsare Nasser Shaer amma bayi cajinsa da wani laifi ba.

Lauyan nasa yace yanzu haka Nasser ya kama hanyar zuwa gida a garin Nablus dake yamma da gabar kogin Jordan.

Jamian tsaron Israilan a ranar 25 ga watan yuni sukayi awon gaba da shugabanin siyasa na Hamas da dama bayan sace wani sojan Israila da yan bindiga sukayi a yankin,haka zalika sun kaddamar da farmaki akan zirin Gaza domin kara matsawa Palasdinawan lamba su saki sojan da suke rike da shi.

Kokarin kasar Masar kuma na ganin an sako sojin ya ci tura.