1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iyaye na gudun rigakafin yara a Ostareliya da Amirka

Yusuf BalaApril 12, 2015

Ana dai samu yara da ke kamuwa da cutar bakon dauro a wasu kasashen na Turai da wasu sassan Amirka saboda kin alluran rigakafi daga iyayen yara.

https://p.dw.com/p/1F6c5
G20 Gipfel Barack Obama und Tony Abbot 15.11.2014
Hoto: Reuters

Firaministan kasar Ostareliya Tonny ya bayyana a yau Lahadi cewa kasar za ta fidda tsarin sanya shinge ga cin moriyar gwamnati ga iyalan da suka ki amincewa 'ya'yansu a yi musu allurar rigakafi.

Wannan tsari na zuwa ne bayan da ake samun iyalai da dama a kasar da basa bari a yi wa 'ya'yansu allluran rigakafi wacce suke cewa tana da hadari ga lafiyar 'ya'yansu.

Wannan yukunuri dai na zuwa ne adaidai lokacin da ake samun bullar cutar kyanda wacce ke da rigakafi a wasu daga cikin kasashen Turai da ma wasu sassan Amirka.

Fiye da yara 39,000 ba a yi musu allurar rigakafin ba a kasar ta Ostareliya.