1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jacob Zuma zai mayar wa gwamnati kudaden da ya waware

March 21, 2014

Shugaban na Afirka ta Kudu yayi amfani da kudaden harajin talakawar kasar wajen kawata wani gidanshi da ke lardin Kwazulu-Natal, abin da ya saba doka.

https://p.dw.com/p/1BTk0
Mandela Trauerfeier Johannesburg 10.12.2013
Hoto: Reuters

Bari mu fara da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda a wannan makon ta leka Afirka ta Kudu inda ta labarto cewa shugaba Jacob Zuma yayi amfani da kudin talakawa wajen kawata wa kansa kasaitaccen gida a garin Nkandla da ke a lardin Kwazulu Natal.

"Rahoton da mai bincike Thuli Madonsela kan almundahana a ma'aikatun gwamnati ta gabatar a ranar Laraba ya gano cewa shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma da iyalansa sun yi amfani da kudaden haraji ba bisa ka'ida ba saboda haka an dole shugaban ya mayar da kaso mafi yawa na kudin da ya yi amfani da su wajen kawata gidansa da suka kai Euro miliyan 17. An karkata kudaden da aka ware wa ma'akatar kula da harkokin jama'a da ta sabunta biranen kasar zuwa yankin na Nkandla. Wannan rahoto ya zo ne a wani lokaci da bai dace ba ga shugaban na Afirka ta Kudu. Domin a farkon watan Mayu za a gudanar da zabuka a fadin kasar, zaben kuma da kusan dukkan cibiyoyin nazarin zabe suka yi hasashen cewa jam'iyyar ANC da ke jan ragamar mulki za ta yi asarar kuri'u da yawa. Hakan ba wai don jam'iyyar ta rasa magoya baya ba ne, a'a sai saboda rashin yarda da ake wa Zuma a matsayin shugaban ANC."

Sojojin Jamus ga kasar Somaliya

Symbolbild - Somalia Nationale Armee
Sojojin gwamnatin Somaliya lokacin atisayeHoto: Getty Images

Rundunar sojan Jamus ta Bundeswehr za ta horas da sojoji a kasar Somaliya inji jaridar Berliner Zeitung tana mai mayar da hankali a kan kudurin da majalisar ministocin Jamus ta zartas na yin wannan aiki a birnin Mogadishu.

"Gwamnatin Jamus za ta tura sojoji kusan 20 zuwa Somaliya a wani bangare na tawagar jami'an horaswa na tarayyar Turai a Mogadishu. A karshen shekarar da ta gabata gwamnatin Jamus ta ki amincewa da shigar da sojojinta cikin tawagar ta EU a Somaliya, saboda a wancan lokaci kasar ta Somaliya na cikin wani mawuyacin hali na rashin tsaro. Yanzu haka dai sojojin Jamus kimanin 560 ne ke aiki a kasashen guda bakwai na Afirka."

Jinkiri wajen hada kan sojojin EU zuwa Bangui

Zentralafrikanische Republik Unruhen
Kokarin tabbatar da zaman lafiya a BanguiHoto: picture alliance/AA

To sai dai yayin da aka samu ci gaba a kokarin girke jami'an sojan da za su ba wa takwarorinsu na Somaliya horon sanin makamar aiki, ita kuwa jaridar die Tageszeitung tsokaci ta yi ga tafiyar hawainiya da ake samu a kokarin hada kan sojojin da za a tura Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wadda ta ce Jamus na daga cikin masu taka wa wannan shiri biriki saboda rikicin Ukraine.

"Shirin girke dakarun kundubala na EU a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya samu jinkiri watakila ma ba zai samu ba. Ko da yake a ranar Litinin ministocin harkokin wajen kasashen EU sun amince da tsarin rundunar da aka wa lakabi da Eufor, amma sun kasa cimma wasu muhimman kudurori bisa manufar girke wannan runduna. A hukumance da kamata yayi rundunar ta fara aiki a wannan mako amma majalisar ministocin ta jadadda cewa ba ta ga muhimmancin gaggauta shirye-shiryen tura dakarun ba. Faransa wadda ke da sojoji kimanin dubu biyu a Afirka ta Tsakiya tana son sauran kasashen Turai su ba da gudunmawa don rage mata nauyin tafiyar da aikin a wannan kasa mai fama da tashe-tashen hankula na kabilanci da addini."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe