1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ignace Murwanashyaka ya mutu

Abdourahamane Hassane
April 18, 2019

Wata kotu a birnin Stuttgart na Jamus ta sanar da cewar jagoran 'yan tawaye na 'yan kabilar Hutu na Ruwanda wanda ake tuhuma da laifin aikata cin zarafin bil Adama a Kwango a shekara ta 2009 ya mutu.

https://p.dw.com/p/3H2Jr
Ignace Murwanashyaka
Hoto: picture-alliance/ dpa

Ignace Murwanashyaka ya rasu a Jamus inda ake tsare da shi a gidan kurkuku inda yake jiran kotu ta sake duba hukuncin da aka yanke masa. Ignace Murwanashyaka wanda ya mutu a wani asibitin jami'ar Mannheim, dan kimanin shekaru 55 kotun ta ce ba ta da bayyanai a game da cutar da ta kasheshi saboda siri na likita. Tun farko kotun Karlsruhe ta yanke wa jagoran na kungiyar mayakan FDLR hukuncin daurin shekaru 13 a shekara ta 20015, bayan da ta sameshi da laifin ba da umurnin kai hare-hare a arewacin Kivu tun a shekara ta 1980.