1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jakadan Faransa ya koma aikinsa a Rome

Yusuf Bala Nayaya
February 16, 2019

Shugaban kasar ta Italiya Sergio Mattarella shi ya karbi jakadan da ke kome a fadar shuban kasa da ke a birnin Rome bayan ya yi kaura saboda zafafan kalamai tsakanin kasashen.

https://p.dw.com/p/3DUqs
Italien - Frankreichs Botschafter nach Streit mit Italien nach Rom zurückgekehrt - Mattarella und Masset
Hoto: picture alliance/AP Photo/P. Giandotti

Jakadan kasar Faransa ya koma kasar Italiya a ranar Juma'a inda ya bayyana cewa kasashen da ke zama makotan juna za su gyatta dangantaka da ke tsakaninsu bayan da suka shiga takaddamada ke zama mai zafi tun bayan yakin duniya na biyu. Shugaban kasar ta Italiya Sergio Mattarella shi ya karbi jakadan da ke kome a fadar shuban kasa da ke a birnin Rome.

Jakada Christian Masset ya ba da sakon wasika ga shugaban kasar ta Italiya  wasikar da ke dauke da sakon gayyatar Shugaba Emmanuel Macron ga takwaransa Mattarella na Italiya zuwa birnin Paris.

A cewar ministar harkokin Faransa a kasashen Turai Nathalie Loiseau, tuni dama shugabannin kasashen biyu sun yi magana ta wayar tarho inda suka jaddada muhimmancin hadin kansu.