Jama'a na cikin wahala a yanki arewacin Mali
November 8, 2012Shugaban ƙungiyar Peter Maurer ya ce tun bayan da ƙasar ta rabu gida biyu a cikin watan Maris da ya gabata ;ayyukan jin ƙaI da suke yi, suka ja da baya ,saboda wahalolin da suke gamuwa da su a yankin na arewaci.
Ya ce mutanen,na buƙatar agaji saboda su ka ɗai karan kansu, ba zasu iya ɗaukar nauyin ɗawainiyar su ba.Nan gaba ne kuma a ranar lahadi mai zuwa aka shirya shugabannin ƙungiyar ƙasashen yammancin Afirka na ECOWAS ,zasu gudanar da wani taro a birnin Abuja na Tarrayar Najeriya domin tantance matakai na ƙarshe a kan yan tawayen na Mali gabannin samun izinin fara kai harin daga MDD.
A ranar talata da ta gabata ne ,man'yan kwamandojin yaƙi na ƙungiyar ƙasashen yammancin Afirka wato ECOWAS ko kuma CEDEAO;suka amince da wani tsari na sake ƙwato yankin arewacin ƙasar Mali ,wanda ke cikin hannu ƙungiyoyin yan tawayen tun watanni takwas da suka wuce .
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu