1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamhuriya Afrika ta tsakiya ta zargi Sudan da kunna mata rikicin tawaye

October 31, 2006
https://p.dw.com/p/Budu

Kakakin gwamnatin Jamhuriya Afrika ta tsakiya, ya zargi hukumomin Khartum da cinna wutar rikicin tawaye a arewancin ƙasar.

Cyriaque Gonda, ya ce sun gayyaci jikadan Sudan a Bangui, domin yayi bayyani a game da dalilan kutsawar yan tawaye, daga Sudan, zuwa Jamhuriya Afrika ta tsakiya.

Idan dai ba amanta ba, a jiya litinin,yan tawayen, suka mamaye garin Biaro, dake tazara kilomita 800 kudancin Bangui.

Taho mu gamar, da ka gwabza, tsakanin su da dakarun gwamnati, ya hadasa mutuwar mutane 12 daga ɓangarorin 2.

Kakakin rundunar tawayen, Captan Abakar sabone,ya ce sun furgaɗi, dakarun gwamnati bayan ɓarin wuta, na kimanin awa guda.

Saidai ya zuwa yanzu, babu wata majiya mai zaman kanta, da ta tabbatar da wannan zance.