1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tana ci gaba da fuskantar matsaloli

March 24, 2014

Gwamnatin wucin gada ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tana ci gaba da neman taimakon kasashen duniya domin shawo kan tashe-tashen hankula

https://p.dw.com/p/1BV7q
Hoto: picture alliance/AA

Shekara guda bayan kifar da gwamnatin Shugaba Francois Bozize ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma murabus da wanda ya gaje shi Michel Djotodia ya yi, har zuwa wannan lokaci ana ci gaba da samun tashin hankali a kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Andre Nzapayeke ke zama firamnistan kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wanda Shugabar gwamnatin wucin gadi Catherine Samba-Panza ta nada, kuma ya tabbatar da kalulaben samar da tsaro cikin kasar, wadda take gab da rushewa sakamakon rikicin da ya rikide ya zama na addini tsakanin Kiristoci masu rinjaye da Musulman kasar. Sannan ya zargi tsohon Shugaba Francois Bozize da hannu cikin tashin hankalin, yayin hira da wannan tasha ta DW:

"Halin da ake ciki yanzu kan ayyukan 'yan anti-Balaka, muna da hujja cewa tsohon Shugaba Francois Bozize yana da hannu a ciki. Akwai tsaffin sojoji a kungiyar, sannan akwai na kusa da tsohon Shugaba Bozize da ke zama 'yan kungiyar anti-Balaka. Wadannan na kusa da Shugaba Bozize ke bayar da karfin gwiwa wa kungiyar, kuma suke neman mayar da tsohon tsarin da zai bai wa Bozize dama ya kammala wa'adinsa kafin karshen wannan gwamnatin wucin gadi. Haka ya nuna akwai hannu a lamarin."

An tura dakarun Faransa da sauran kasashen Afirka domin kare kasar daga wargajewa lokacin da lamura suka kazance. Wani abu shi ne tsohuwar gwamnatin Michel Djotodia ta fara bincike bisa hannu tsohon Shugaban Francois Bozize kan tashin hanklin da ake samu, shin ina aka kwana?

Französische Truppen in Zentralafrika
Hoto: picture-alliance/dpa/ECPAD

"Binciken yana gudana. Tun ranar 5 ga watan Disamba abubuwa sun sauya. A lokacin da aka fara bincike sai lamura suka sauya, 'yan anti-Balaka suka tayar da kayar baya. An aikata manyan laifuka na kisan kai, da ta'addanci da kashe-kashe a Bangui da sauran yankunan kasar."

Wata matsala ita ce yadda ake samun 'yan anti-Balaka da ke ci gaba da hallaka Musulmai a cikin kasar. Firaminista Andre Nzapayeke ya kara da cewa kasar Jamhuriyar Afirka Tsakiya bata nuna kyama wa Musulmai. Sannan ya yi tir da masu kai wa Musulmai hare-hare, inda ya ce barayi ne masu aikata laifuka. Wani abu mai mahimmaci shi ne tabbatar da doka da oda, amma zuwa wannan lokacin gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya za iya mayar cikekken zaman lafiya:

"Maganar tsaro ita ce magana ta farko da gwamnatin wucin gadi ke ba da fifiko a kai."

Firaminista Andre Nzapayeke ya kuma nuna mahimmancin kasashe masu ba da taimako kamar kasar Jamus, wadda ministan kula da raya kasashe Gerd Muller ya kai ziyara, sannan kungiyar GIZ ta kulla hulda domin kawo ci-gaba wa kasar. Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tana kan neman taimakon kasashen duniya domin kawo karshen matsalolin tashe-tashen hankula da suka rikita kasar.

Firaminista Andre Nzapayeke
Firaminista Andre Nzapayeke na Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: I.Sanogo/AFP/GettyImages

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta fada cikin rudani tun lokacin da 'yan tawaye Seleka suka kifar da gwamnatin Shugaba Francois Bozize, inda Michel Djotodia ya dauki madafun iko. Amma an tilasta wa Djotodia ajiye aiki ranar 10 ga watan Janairu na wannan shekara ta 2014, saboda kasa magance yanayin da aka shiga na tashe-tashen hankula masu nasaba da addini.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar