1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami´an tsaro a Masar na matsa kaimi ga kamun yan uwa musulmi

November 30, 2005
https://p.dw.com/p/BvIh

Gwamnatin kasar Masar, na matsa kaimi ga kame- kamen membobin kungiyar yan uwa musulmi, a jajibirin zagayen karshe, na zaben yan majalisun dokoki.

A tsukin makwani 2, da su ka wuce, jami´an tsaro, sun capke a kalla mutane 600, membobin wannan kungiyar.

Ya zuwa yanzu, sun sallami da dama daga cikin su, saidai kuma su na ci gaba, da kame wasu sabi.

Kungiyar yan uwa musulmi, ta taka kyawkaywar rawa, a zabbukan yan majalisun dokokin kasar Masar, tare da lumkawa har so biyar, yawan yan majalisun su, a majalisa mai barin gado.

Kakakin kungiyar, ya zargi gwamnati da aikata,wannan kame kame, barkatai, don rage kaifin niyar, da jam´ar kasa ta dauka, ta baiwa kungiyar nasara, a zagaye karshen na zaben.