1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'iyyu takwas sun kulla sabon kawance a Nijar

Abdul-raheem Hassan
July 17, 2017

Shugabannin jam'iyun hadakar ta 'yan ba ruwana wato FPNAD, suna bayyana yin tsayin daka domin yin fafutukar maido da mulkin demokradiya da ya shiga wani halin karan tsaye.

https://p.dw.com/p/2gf6O
Niger Niamey Opposition
Hoto: DW/M. Kanta

Shugabannin jam'iyun sun lashi takobin yin fafutuka wajen kare hakkin 'yancin yan  Adam da ma matsalolin tattalin arziki da Nijar ke fama da su wanda suke ganin ya jefa shakku a kan mokamar demokradiya. gungun kawancen sun koka kan yadda mahuntan Nijar ke kame 'yan jarida a fadin kasar. 

Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou Hoto: F. Batiche/AFP/Getty Images

To sai dai jam'iyyar Modern Ma'aikata sun nesanta kan su da wannan sabuwar hadaka, yayin da ita ma jam'iyyar PNDS mai mulki ta shugaba Mahamadou Issoufou ta zargi sabuwar hadakar da nufin kulla jam'iyyar adawa a maimakon akidar da suka kira kan su na 'yan ba ruwana.

Sabuwar kungiyar da ya hada jam'iyyu sama da 12, sun ce ba su da niyar zama 'yan amshin shatan gwamnati ko jam'iyyun adawa, amma suna fatan fidda dan takara guda da za su mara wa baya a babban zaben kasar da ke tafe.