1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam´iyar Firaministan Estonia, Andrus Ansip ta lashe zaben ´yan majalisar dokoki

March 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuQc
Hukumar zabe ta kasar Estonia ta ce jam´iyar canji dake jan ragamar mulki ta lashe zaben ´yan majalisar dokoki wanda ya hada har da kada kuri´a ta hanyar intanat. Alkalumma sun yi nuni da cewa jam´iyar FM Andrus Ansip ta samu kashi 27.8 cikin 100 na yawan kuri´un da aka kada yayin da abokiyar kawancen ta ta samu kashi 26.1 cikin 100. To amma FM Ansip ya yi nuni da cewa zai nemi kulla sabon kawance da jam´iyar masu ra´ayin mazan jiya, wadda ta zo ta uku a zaben da kashi 17.9 cikin 100. Kimanin kashi 60 cikin 100 na wadanda suka cancanci kada kuri´a a kasar suka shiga zaben na jiya wanda shi ne na farko da kasar dake yankin Baltic ta gudana tun bayan shigar ta KTT da ta NATO a shekara ta 2004. Zaben shi ne kuma na farko a duniya baki daya da aka amince masu zabe suka kada kuri´a ta intanat.