1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu mulki sun yi rinjaye a zaɓen Burundi

Yusuf BalaJuly 7, 2015

Wannan sakamako dai na zuwa ne duk da ƙauracewar da 'yan adawa suka yi a zaɓen da ƙungiyoyi na ƙasa da ƙasa haɗi da Majalisar Ɗinkin Duniya da ke cewa zaɓen bai cika ba.

https://p.dw.com/p/1FuA5
Burundi Präsident Pierre Nkurunziza
Shugaba Pierre NkurunzizaHoto: Getty Images/AFP/F.Guillot

Jam'iyyar da ke mulki a ƙasar Burundi ta shugaba Pierre Nkurunziza ta lashe mafi rinjayen kujerun majalisar ƙasar a zaɓen mai cike da ruɗani.Hakan ya bayyana ne a cikin wani sakamako da hukumar zaɓen ƙasar ta fitar a ranar Talatan nan.

Jam'iyyar ta CNDD-FFD ta shugaba Nkurunziza da ke neman tazarce a karo na uku a zaɓen ƙasar da ke tafe, ta samu nasarar lashe kujeru 77 daga cikin 100 na majalisar, a cewar hukumar zaɓen ƙasar.Wannan sakamako dai na zuwa ne duk da ƙauracewar da 'yan adawa suka yi a zaɓen da ƙungiyoyi na ƙasa da ƙasa hadi da Majalisar Ɗinkin Duniya suka ce bai cika sharuƊa ba na zama sahihi.