1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar Swapo a Namibiya na fuskantar kalubale

Mohammad Nasiru Awal SB
November 27, 2019

An fara kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a Namibiya da ke kudancin Afirka, inda shugaban kasa Hage Geingob ke fuskantar kalubale.

https://p.dw.com/p/3Tp37
Namibia Wahlen Parlamentswahlen Präsidentschaftswahlen
Hoto: AFP

A kasar Namibiya an bude rumfunar zabe a zabukan shugaban kasa da na wakilan majalisar dokoki inda jam'iyyar da ke jan ragamar mulki ke fuskantar kalubale mafi girma tun bayan samun 'yancin kan kasar kusan shekaru 30 da suka gabata.

Kimanin mutum miliyan 1.3 aka yi wa rajistar zabe a kasar mai dimbin arzikin karkashin kasa da ke yankin kudancin Afirka.

Duk da koma-bayan tattalin arziki da matsaloli na cin hanci da rashawa da kuma fari, an yi hasashen cewa jam'iyyar da ke jan ragama ta Swapo za ta lashe zaben. Shugaban kasa Hage Geingob mai shekaru 78 na jam'iyyar ta Swapo da ke fuskankantar kalubale daga 'yan takarar 10 ciki har da mace a karon farko da kuma wani dan jam'iyyarsa, yana neman wa'adin mulki na biyu.