1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar gwamnati ta sha kaye a Jamus ta Yamma

Usman Shehu Usman MA
May 16, 2022

Zaben da ya gudana a jiya a jihar North Rhine-Westphalia a Jamus, gwaji ne ga tasirin 'yan siyasar kasar kasancewar shi ne zaben farko tun bayan da aka samu sauyin gwamnati.

https://p.dw.com/p/4BN1q
Deutschland | Landtagswahl NRW | Hendrik Wüst
Hoto: Tobias Schwarz/AFP/Getty Images

Sakamako dai da aka samu bai yi dadi wa sauran jam'iyyu da suke cikin kawance na SPD da FDP ba. Wannan ya nuna cewa dole cikin babbar jam'iyyar kawance ta shugaban gwamnati ya duri ruwa.

Jam'iyyar SPD ta shugaban na gwamnatin Jamus, ta samu mummunan koma baya a zaben na jihar North Rhine-Westphalia. Jam'iyyar ba ta taba samun mummunan faduwa a tarihinta a jihar kamar a wannan zabe ba. Domin tun shekaru 75 da suka gabata jam'iyyar ba ta samun kasa da kashi 30 cikin dari, amma a zaben na ranar Lahadi ta samu kashi 18 cikin dari ne kacal, kuma wannan zabe ne da ya fi mahimmanci a bana.

A gargajiyance zaben jihar shi ne ke zama tamkar karamin zaben Tarayya a Jamus baki daya. Wadanda dai za a iya cewa suka yi babbar nasara a zaben su ne jam'iyyun CDU da ke mulki a jihar da kuma jam'iyyar kare muhalli ta the Green. Domin ita kam jam'iyyar The Green wacce ta samu kashi 18 cikin dari, wanda shi ne mafi yawan kuri'u da ta samu a dukkan zabuka biyu na baya.

Landtagswahl in Nordrhein-Westfalen - CDU-Wahlparty - Hendrik Wüst
Hoto: Rolf Vennenbernd/dpa/picture alliance

Kuma a gwamnatin jihar ma dai dole sai a samu sauyi, domin jam'iyyar kawance a baya ta FDP ta samu mummunan kaye, inda shugabanta na kasa Christian Lindner ya kwatanta sakamakon zaben a matsayin wani mummunan koma baya da kuma yammaci ne na makoki.

Babban abin da wannan zaben ya nunar dai shi ne babbar jam'iyar SPD a cikin kawance da ke mulki a kasar karkashin jagorancin Olaf Schulz ta na da jan aiki a gabanta na sake shawo kan Jamus a harkokin cikin gida da na waje musamman yakin UKraine. Ita kuwa jam'iyyar kare muhalli the Greens da shugabanninta a yanzu sun samu matukar kwarin gwiwar cewa jam'iyarsu fa a ba karamar jam'iyya ce ba, amma jam'iyyace da ta karbu a kananan hukumomi zuwa jihohi har ma a Tarayya.