1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Taraba: Martanin kungiyoyin mata

UWais Abubakar Idris / LMJNovember 9, 2015

A Najeriya kungiyoyin rajin kare hakokin mata sun mayar da martani dangane da samun mace ta farko da ta zama gwamna a kasar, biyo bayan soke zaben gwamnan jihar Taraba.

https://p.dw.com/p/1H2Vn
Hoto: DW/K. Gänsler

Kotun sauraron kararrakin zabe da ke zamanta a Abuja fadar gwamnatin Najeriya dai ta ayyana Sanata Aisha Jummai Alassan a matsayin wadda ta lashe zaben bayan da ta soke zaben gwamnan da aka gudanar cikin watan Maris din da ya gabata. A natabangaren jamiyyar PDP da kotu ta rusa zaben da ta ci a jihar ta bayyana cewa za ta daukaka kara domin kalubalantar hukuncin.

Asarar kujerun gwamna

PDP dai ta yi asarar kujerar gwamnan jihar Rivers da jihar Akwa Ibom da kotu ta soke zaben kananan hukumomi da dama, abin da ya sa jamiyyar shiga hali na rashin natsuwa, a yanzu kuma ga jihar Taraba inda kotun sauraren kararrakin zabe ta rusa zaben gwamman jihar Darius Ishaku na jmiyyar PDP tare da baiwa Aisha Jummai Alhassan ta jamiyyar APC nasara.

Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Duk da cewa a bayyane take a fili jamiyyar ta PDP ta fusata da hukuncin ganin cewa sannu a hankali tana neman rasa ‘yan jihohin da suka kasance mata matyafi a yankin arewacin Najeriya, abin da ya sanya jamiyyar bayyana cewa za ta nufi kotu don kalubalantar soke zaben da kotu ta yi a Abuja. To ko wane kwarin guiwa suke da shi da za su nufi kotu a yanzu. Barrsiter Abdullahi Jallo shi ne mataimakin sakataren jamiyyar ta PDP ya kuma ce:

"Wani abu da nake son mutane su sani ba kamar yadda wani ya ce PDP ta karya dokokinta ba. Mun nufi kotun daukaka kara in bamu gamsu ba mu nufi kotun koli, a nan kada wani ya ce an kwace don ba'a san maci tuwo ba sai miya ta kare."

Murnar kungiyoyin kare hakkin mata

Tuni dai kungiyoyin rajin kare hakkin mata a Najeriya suka shiga tsalle suna murna a kan abinda suke ganin kafa tarihi ne a guguwar siyasar da ke kadawa a Najeriyar, musamman dadewar da suka yi suna kokarin ganin ana damawa da su a mulkin da suka yi amannar cewa sune suka fi fitowa zabe. Hajia Saudat Mahdi ita ce shugabar kungiyar kare hakokin mata ta WRAPA ga kuma abin da ta ke cewa:

"Allah ya yi mana adalci, gaskiya ta tabbata kuma muna kyautata zaton cewa wannan al'amarin ya zama zakaran gwajin dafi, wannan zai kara karfi a matsayinmu na mata mu san cewa adalci a wajen ubangiji shi ne abin dogaro, kullum muna cewa yawan mutane shine kasuwa."

Dandazon mata a Najeriya yayin babban zaben kasar
Dandazon mata a Najeriya yayin babban zaben kasarHoto: DW/Z.Rabo

Ga sauran matan Najeriya dai suna cikin hali na annashuwa cike da kyakyawan fata a kan sakamakon da ya kai ga samun mace ta farko a matsayin gwamna a kasar. A yayin da matan ke cikin murna dai abin jira a ganin shi ne sakamakon da zai biyo bayan daukaka karar da jamiyyar PDP da ma gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku da aka soke zabensa, wanda shi ne zai tabbatara da nasarar matan na Najeriya.