1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar PJC a Libiya ta janye daga gwamnati

January 21, 2014

Jam'iyyar masu kishin addini ta PJC wacce ke fafutukar samar da shari'a da ci-gaba, ta janye ministocinta biyar daga gwamnatin Ali Zaidan

https://p.dw.com/p/1AutF
Libyen Nationalversammlung in Tripolis
Hoto: MAHMUD TURKIA/AFP/Getty Images

A cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta bayyana ta ce ta ɗora alhakin abin da zai biyo baya ga jam'iyyun siyasar da ke goyon bayan gwamnatin, Waɗanda suka taimaka ga samun rinjaye a ƙuri'ar ƙin yanke ƙauna ga gwamnatin da aka kaɗa a gaban majalisar dokokin ƙasar.

Jam'iyyar tana zargin gwamnatin Ali Zeidan da gazawa wajen shawo kan matsalolin na rashin tsaro da ake fama da su, kuma tana da ministoci guda biyar a cikin majalisar ministocin guda 32. Waɗanda suka haɗa da na tattalin arziki da muhali, da wasannin motsa jiki,da na man fetur da samar da wuta lantarki.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu