1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyun adawa 10 sun yi hadaka a Nijar

Mahaman kanta/A'RaheemSeptember 1, 2016

Kawancen jam'iyyun adawa a Nijar sun kulla kwancen kalubalantar jam'iyya mai mulki da rashin iya gudanar da tsarin shugabanci.

https://p.dw.com/p/1JtgF
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Shugaban kasar Nijer, Muhamadou IssoufouHoto: F. Batiche/AFP/Getty Images
Shuwagabannin jam'iyyun da suka yi hadaka da nufin yin adawa a Nijar, sun koka kan yadda lamuran siyasar kasar ke tafiya da ma take dokoki da ke hannun riga da tafarkin dimokradiyya. Wadannan dalilai ne da suka tinzirasu kawancen adawan kirkirko da babbar jam'iyyar hadaka da za ta ba su damar hadewa karkashin inuwa guda dan kawo sauyin lamuran da suka shafi dimokradiyyar kasar.
Niger Niamey Opposition
Hoto: DW/M. Kanta
Jam'iyyun da suka hade wuri guda sun sawa kwancen jam'iyyun suna FRDDR, wanda za su kwalubalanci jam'iyya mai ci yanzu. Wannan kawance dai na zuwa ne bayan da babbar kawar su jam'iyyar MNSD Nasara ta Alhaji Seini Oumar ta sauya sheka zuwa gwamnatin shugaba Mahamadou Issoufou.
A nasu bangaren gwamnatin Nijar sun ce suna maraba da wannan hadaka, amma suna fata jam'iyyun kawancen da su rik sara suna duban bakin gatari wajen kare dokoki da 'yancin 'yan kasa a yayin da suke daura damarar yin adawa da nufin kalubalantar jam'iyya mai mulki a kasar.
Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani