1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar Die Linke ta samu nasara a zaben Thuringia

Abdourahamane Hassane
March 5, 2020

A karshe, an zabi Bodo Ramelow na jam'iyyar Die Linke a zagaye na uku na zaben Thuringia da ke a gabashin Jamus bayan da abokin karawarsa dan takarar jam'iyyar AFD ta masu kyamar baki Bjorn Höcke ya janye takararsa.

https://p.dw.com/p/3YtOf
Thüringen Erfurt Landtag Vereidigung Ministerpräsident Ramelow Die Linke
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Meyer

Jamiyyar ta Die Linke ta samu goyon bayan jam'iyyun siyasar na SPD da kuma masu fafutukar kare muhali. Sai dai jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta kauracewa ba da goyon baya ga jam'iyyar ta Die Linke saboda alakar da ta ce ta yi a can baya da jam'iyyar 'yan Nazi. A zaben farko da aka yi a jihar a cikin watan jiya kafin a sake shi, dan takarar jam'iyyar FDP Thomas Kemmerich ya samu nasara da goyon bayan jam'iyyar AFD da kuma CDU abin da ya janyo rikicin siyasa a Jamus din har wanda aka zaban ya yi marabus.