1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ba ta fargabar kutsen Rasha a zabe

Yusuf Bala Nayaya
May 2, 2017

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana cewa ba ta da wata fargaba a dangane da batun zargin yin kutsen kasar Rasha kan al'amuran zaben kasar da ke tafe a watan Satumba mai zuwa.

https://p.dw.com/p/2cExa
Russland | Pressekonferenz Merkel Putin
Hoto: Getty Images/AFP/A. Nemenov

Merkel ta bayyana haka ne a yayin ziyarar da ta kai kasar ta Rasha a lokacin da take amsa tambayoyin manema labarai. Har ila yau ta ce ita mace ce da ba ta azarbabi, za ta yi yakin neman zabe cikin nutsuwa domin jan hankalin magoya baya. A nasa bangaren Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya shaida wa Merkel cewa, ya na fata za su ci gaba da tattauna batutuwa da suka hadar da rikicin gabashin Ukraine da yakin basasar Siriya. A yayin fara tattaunawar tsakanin shugabannin biyu, Shugaba Putin ya ce za su yi amfani da wannan dama su tattauna kan dangantakar da ke tsakaninsu da sauran batutuwa da ke zame musu alakakai, abin da Merkel ta ba shi amanna tana mai cewa:

"Tabbas zamu tattauna kan batutuwa na kasa da kasa da suka hada da halin da ake ciki a Ukraine da Siriya da kuma Libiya. Zan kuma yi farin ciki wajen tattauna batun dangantakar da ke tsakaninmu."