1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da Amirka sun shirya tinkarar matsalolin duniya

Zulaiha Abubakar
November 8, 2019

A wata ganawar da ta wakana da tsakanin hukumomin Jamus da na Amirka, kasashen biyu sun lashi takobin hada karfi don tinkarar lamura masu sarkakiya a wasu kasashe.

https://p.dw.com/p/3SifN
Offizieller Besuch des US-Außenministers Pompeo in Deutschland
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Angela Merkel ta daukar wa Amirka alwashin ci gaba da bayar da hadin kai da agaji a bangaren samar da zaman lafiya a yankunan da ke fama da rikici, yayin da Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya kai mata ziyarar aiki a birnin Berlin a wannann Juma'ar.

Angela Merkel ta lissafo kasashen da suka hada da Afghanistan da Siriya da Libya da kuma Ukraine a matsayin misalin kasashen da Jamus ta taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da zaman lafiya.

A nasa bangaren sakatare Pompeo ya jinjina wa shugabar gwamnatin Jamus din tare da bayyana tarayyar Jamus a matsayin aminiyar Amirka.

Pompeo ya bukaci Jamus ta yi watsi da alakar sadarwa yada bayanai da kamfanin sadarwa na Huawei, bukatar da nan take Merkel din ta ki amincewa.

Alaka tsakanin kasashen biyu dai ta yi rauni tun bayan darewar Shugaba Donald Trump shugabancin kasar Amirka.