1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Jam'iyyar SPD ta sha kaye a Berlin

February 12, 2023

Jam'iyyar Social Democrats ta sha kaye a zaben da aka gudanar na jiha a Berlin, inda kiyasin kafafen yada labarai ya nunar da cewa SPD din ce ta zo ta biyu a zaben.

https://p.dw.com/p/4NOP9
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Clemens Bilan/Getty Images

Jam'iyyar shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ta Social Democrats ta sha kaye a zaben da aka gudanar na jiha a Berlin, inda kiyasin kafafen yada labarai ya nunar da cewa SPD din ce ta zo ta biyu a zaben. Jam'iyyar 'yan mazan jiya ta tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Christian Democratic Union wato (CDU) ce ta lashe kaso 28 cikin 100, na kuri'un da aka kada a zaben 'yan majalisun dokoki na jihar ta Berlin.

Rahotanni sun nunar da cewa jam'iyyar SPD ta shugaban gwamnati Olafa Scholz ta samu kaso 18 cikin 100 ne kacal, abin da ke zama rashin nasara mafi muni da ta yi a zabe tun bayan yakin duniya na biyu, kamar yadda kiyasin kafafen yada labaran Jamus din na ARD da ZDF ya nunar.