1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ma na sanya ido kan E-Mails da wayoyin tarfo

June 26, 2013

Matakan leken asiri da hukumomin leken asirin kasashen ketare ke dauka, sun zo wa da yawa daga cikin Jamusawa da mamaki.

https://p.dw.com/p/18x5u
ARCHIV - Netzwerkkabel stecken in Berlin in einem Verteiler für Internetverbindungen (Archivfoto vom 11.12.2008). Deutsche Regierungs- und Behördennetze sind zunehmend Ziel ausländischer Spionageangriffe, vor allem aus China. Von Januar bis September dieses Jahres seien rund 1600 Attacken auf Computer und Großrechner festgestellt worden, sagte der Sprecher des Bundesinnenministeriums, Stefan Paris, am Montag (27.12.2010) in Berlin. Zum Vergleich: Im ganzen Jahr 2009 waren es insgesamt 900 Angriffe. Foto: Arno Burgi (zu 4271 vom 27.12.2010) +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture alliance/dpa

Sai dai a cikin kasar ta Jamus ma hukumomin tsaron kasar na kokarin fadada matakan sanya ido a kan hanyoyin sadarwa na Internet wato kamar sakonnin E-Mails da kuma na waya. Sai dai kuma suna fuskantar turjiya ta shari'a.

Sakonnin E-Mails da SMS da kuma sauran sakonni na wayoyi kimanin miliyan 37 ne hukumar leken asirin Jamus ta BND ta tattara a shekarar 2010. Wani rahoto da kwamitin sanya ido kan hanyoyin sadarwa na majalisar dokokin Jamus ya bayar ya yi nuni da cewa bayanan da aka tattara a bangaren yaki da ta'addanci a shekarar ta 2010 sun kai miliyan 10. Sai dai yanzu haka wannan adadi ya ragu, inda a bara ya kai dubu 900.

Tattara bayanai don kare kasa

Aikin hukumar ta BND shi ne tattara bayanai domin kare Jamus daga wata barazana daga ketare. Hukumar na bincike a kan ayyukan ta'addanci da cinikin makamai ba bisa ka'ida ba da aikace-aikacen masu fataucin dan Adama da masu jigilar mugan kwayoyi. Duk wani aiki na yi wa jama'a leken asiri sai hukumar ta BND ta bi tsauraran dokokin kasar wanda kuma wasu 'yan majalisar dokoki ke sa wa ido.

SPD Bundestagsabgeordneter Michael Hartmann
Michael Hartmann na jam'iyar SPDHoto: Deutscher Bundestag / Lichtblick/Achim Melde

Michael Hartmann memba ne a kwamitin majalisar dokoki dake sanya ido kan hanyoyin sadarwa na zamani ya amsa cewa ko da yake hukumar BND ta fadada ayyukanta zuwa fasahohin dijital, amma ba wai an sakar wa hukumar leken asirin wuka da nama ba ne.

"Hukumar na takatsantsa a binciken da take yi, kuma ba ta gaggawar duba bayanan komin yawansu har sai da kwakkwarar shaidar cewa Jamus na fuskantar wata barazana ta kawo mata hari. Ayyukanmu sun bambamta kwarai da wanda Amirkawa ke yi. Ga misali ba za mu iya yi wa kasashe kawayenmu leken asiri ba."

Hukumomin leken asirin Jamus a ta bakin Hans-Peter Uhl memba a kwamitin majalisar dokoki ba sa sauraron hirarrakin jama'a ta wayoyin tarfo har sai da wata shaida mai gamsarwa. Idan ma abokin hirar bako ne to ana share hirar kuma a rubuta a kan takarda ta yadda hukumomin kare bayanan Jama'a za su iya ganin idan bukatar haka ta taso.

Kare 'yancin 'yan kasa

Hukumomi dai na bukatar amincewar kotu kafin su saurari hirarrakin domin girmama zaman jama'a abu ne dake da muhimmanci ga dukkan mazauna wannan kasa kuma ke samun kariya daga kundin tsarin mulkin kasar.

Gisela Piltz Bundestag Abgeordnete FDP Archiv 2011
Gisela Piltz ta FDPHoto: Imago

Dokokin Jamus dai sun ba da umarni da a sanar da duk wanda aka yi wa leken asiri bayan kammala wannan mataki, abin da hukumomin leken asirin ke yi. Sai dai hakan na janyo korafe-korafe da dokokin Jamus din suka amince da su, kamar yadda Gisela Piltz memba a kwamitin majalisar dokokin ta yi karin bayani.

"Muna da jerin korafe-korafe da aka gabatar wanda kuma muka dora wa sakatariyar kwamitin nauyin kula da su. Amma a wasu daidaikun batutuwan mu da kanmu ne ke nazari a kai. Kawo yanzu dai ban ga wani lamari dake nuna cewa hukumomin leken asirin sun wuce gona da iri ba."

A cikin rahoton baya-bayan nan da kwamitin sanya idon kan hanyoyin sadarwa na majalisar dokokin Jamus ya bayar, ya nuna cewa daga cikin sakonnin E-Mails sama da miliyan 2.5 da hukumar leken asiri ta BND ta yi bincike a kai, 300 kadai ne ke kunshe da bayanai masu muhimmanci. A saboda haka ne masana ayyukan ta'addanci ke kira da a sabunta ayyukan hukumar yadda za su dace da zamani domin an ce wai karen bana shi ne maganin zomo bana.

Mawallafa: Wolfgang Dick / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu