1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Muhimmancin tallafa wa kasar Mali

April 7, 2017

Gwamnatin kasar Jamus ta bayyana muhimmancin kai dauki ga kasar Mali da ke yammacin Afirka da ke fama da rikice-rikice.

https://p.dw.com/p/2atq9
Mali Sigmar Gabriel in Bamako
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel da takwaransa na Faransa Jean-Marc Ayrault sun kai ziyara a garin Gao da ke arewacin kasar Mali don duba irin gudummawar da kasashensu ke bayarwa wajen tabbatar da tsaro da kyautata zaman al'uma a yankin  mai fama da rikice-rikice 'yan tarzoma.

A lokacin da yake magana da manema labari a wannan Juma'ar, ministan harkokin wajen Jamus Sigma Gabriel ya ce aikin tawagar kasa da kasa a Mali yana da muhammanci ga yankin da ma nahiyar Turai baki daya.

Ya ce:

"Wannan yanki babbar tunga ce ta rikice-rikice, musamman ta'addancin da ke haddasa zaman hijira da kaurar jama'a. Mali kasa ce kuma mai fama da matsanancin talauci, inda matasa ke rasa makoma ta rayuwa, saboda haka ya zama wajibi mu taimaka.  Kyakkyawar alama ce yanzu yadda aka samu hadin kai a Turai musamman tsakanin Jamus da Faransa bisa manufar kawo dauki."