1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na inganta huldar ta da Afirka

Mohammad Nasiru Awal A H
August 28, 2018

Dangantaka tsakanin Jamus da kasashen Afirka da sake bullar cututtuka a jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango sun dauki hankulan jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/33t96
Deutschland G20 Afrika Treffen
Hoto: Getty Images/AFP/J. Macdougall

Jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi kasar Ruwanda na daga cikin jerin kasashen Afirka da a baya bayan nan gwamnatin tarayyar Jamus ke kokarin inganta hulda da ita musamman a manufofin Jamus kan nahiyar Afirka. Jaridar ta ce Ruwanda da ke zama karamar kasa a gabashin Afirka ta samu bunkasar tattalin arziki bayan kisan kare dangi na 1994, ta gina hanyoyi, gwamnati ta haranta amfani da jakunan leda sannan an tilastawa kowane dan kasa da ya tsabtace muhallnsa sau daya a wata. Kasar tana da yawan mata a majalisar dokoki fiye da sauran kasashen duniya sakamakon matakin Shugaba Paul Kagame na tallafa wa mata. Saboda haka ga ministan raya kasashe masu tasowa na Jamus Gerd Müller, wanda a wannan Alhamis ya fara rangadin wasu kasashe bakwai na Afirka, Ruwanda na zama abin koyi ga sauran kasashen nahiyar, musamman a dangane da manufofin Jamus da suka shafi Afirka. Kasashen da ministan zai kaiwa ziyara sune Eritriya, Habasha, Botswana, Zimbabuwe, Mozambik, Ghana da kuma Chadi.

Präsident Ruanda Paul Kagame
Shugaban kasar Ruwanda, Paul KagameHoto: Imago/Zumapress/E. Contini

Ita ma jaridar Berliner Zeitung ta buga labari dangane da huldodi tsakanin Jamus da Afirka inda ta mayar da hankali kan ziyarar da shugaban kasar Angola Joao Lourenco ya kawo birnin Berlin a wannan mako. Jaridar ta ce gwamnatin Jamus da 'yan kasuwar kasar sun yi wa Angola alkawarin saka hannu jari na miliyoyi dubbai na Euro a harkokin aikin gona da gina hanyoyi da fasaha. Angola ita ce kasa ta biyu mafi fitar da man fetir bayan Najeriya a Afirka, amma tana fama da matsalar faduwar farashin kayayyaki. Kasar na fadada hanyoyin da za ta rika samun kudin shiga da sauran huldodi da wasu kasashe ciki kuwa har da neman masu zuba jari daga Jamus.

Shugaban kasa ya rasa ta inda zai faro dangane da matsalolin da ke gabanshi, inji jaridar die Tageszeitung a labarin da ta buga kan kasar Mali. Ta ce a Mali shugaba Ibrahim Boubacar Keita ne ya yi nasara lashe zaben shugaban kasar sai dai bisa ga dukkan alamu zai yi rauni a wa'adin mulkinsa na biyu. Matsalolin rashin tsaro da aikace-aikacen kungiyoyin 'yan bindiga da ake fama da su har yanzu a arewaci da tsakiyar Mali na daga cikin kalubalen da ke gaban gwamnati, amma ba ta da karfin magance matsalolin.

Kongo Ebola
Jami'an kiwon lafiya a jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: picture-alliance/AP Photo/J. Bompengo

A karshe sai jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta leka kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango tana mai cewa annoba ta dawo. Ta ce baya ga cutar Ebola yanzu haka cututtukan Cholera da Polio sun barke a wasu yankuna na Kwango, lamarin da ya kara dagula mawuyacin halin da ake ciki a kasar. Alkaluma da ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta bayar na nuni da cewa Cholera ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 125 sannan ana yi wa wasu 2100 jinya, yayin da akalla mutunm 60 suka rasu sakamakon cutar Ebola da ta barke a gabashin kasar a wannan wata na Agusta.