1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na tanadin dokoki bayan Brexit

Abdul-raheem Hassan
January 18, 2019

Dokar na fatan fayyace makomar Jamusawa mazauna Birtaniya da 'yan Birtaniya da ke zama a Jamus idan aka cimma Brexit za ta ba wa 'yan Birtaniya damar neman izinin zama 'yan Jamus.

https://p.dw.com/p/3Bkph
Feierstunde 100 Jahre Frauenwahlrecht im Bundestag
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Sabuwar dokar ta samu amannar kusan yawancin wakilan jam'iyyun siyasa a majalisar dokokin Bundestag in ban da jam'iyyar AfD, za ta ba wa 'yan Birtaniya mazauna Jamus kusan dubu 120 damar neman izinin zama 'yan kasa kamin kammala shirin ficewra Birtaniya daga EU nan da 2020. Jamusawa da ke son izinin zama 'yan Birtaniya na da damar cimma burinsu kamin kammala shirin Brexit, sai dai ba kasafai dokokin Jamus ke ba da damar mallakar izinin zama dan kasashe biyu ba.