1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta ba wa Najeriya tallafi a fannin tsaro

Yusuf Bala Nayaya
December 19, 2016

Jamus ta bayyana cewa za ta kashe kudi da ya kai miliyan 230 na Euro daga shekarar 2016 zuwa 2017 kan irin wadannan ayyuka a kasashen na Jodan daTunisiya da Najeriya da Nijar da Mali.

https://p.dw.com/p/2UUnO
Nigeria von der Leyen in Abuja
Ministar tsaron Jamus Von der Leyen a tsakiya lokacin da ta sauka Abuja NajeriyaHoto: picture alliance/dpa/K. Nietfeld

Ministar tsaron kasar Jamus Ursula von der Leyen a ranar Lahadi a Najeriya ta bayyana alkawarin samar da tallafi da ya kai na Euro miliyan hudu da dubu dari biyu a tallafin kayan aikin soji a wani bangare na kokari na dasa aya ga yunkurin masu son barin kasashen Afirka zuwa Turai.

Ministar tsaron ta je birnin Abuja fadar gwamnatin Najeriya don fara aikin mika kayayyakin da suka hadar da na'urorin samar da bayanan soji da na'urar gano kananan bama-bamai da ake binnewa 180  da asibitoci na tafi da gidanka da za a iya dauka daga wuri zuwa wuri don bayarwa ga wannan kasa da ta ga gallaba ta ayyukan 'yan ta'addar Boko Haram.

A ranar Litinin din nan ce dai ake sa ran von der Leyen za ta ci gaba daga Najeriya ta tafi zuwa kasar Mali a ci gaba da rangadin da ta ke yi a wadannan kasashe na Afirka.