1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta damu lafiyar dan adawar Chaina Liu Xiaobo

Gazali Abdou Tasawa
July 12, 2017

Gwamnatin Jamus ta yi kira ga mahukuntan Chaina da su kyale Liu Xiaobo fitaccen dan adawar kasar ya fice zuwa neman magani a kasashen waje,

https://p.dw.com/p/2gP29
Liu Xiaobo
Hoto: picture-alliance/AP

Gwamnatin Jamus ta yi kira ga mahukuntan kasar Chaina da su kyale Liu Xiaobo fitaccen dan adawar kasar ya fice zuwa neman magani a kasashen waje, kana ta ce a shirye take ta karbe shi domin yi masa maganin. 

Liu Xiaobo dan shekaru 61 wanda ya taba samun kyautar zaman lafiya ta Nobel na fama da cututukan daban daban da suka hada da matsalar nunfashi da cutar daji wadanda ke bukatar kulawa ta musamman. Sai dai mahukuntan kasar ta Chaina sun yi watsi so tari da bukatarsa ta ganin sun ba shi dama ya tafi kasashen waje domin samun magani, matakin da ake fassara wa da tsoron da mahukuntan Chainar ke yi na ganin dan adawar da ya yi fice wajen cancakar gwamnatin kasar ya sake samun dama ta ci gaba da sukar lamirin nata a kasashen ketare,