1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta gano wasu masu kutse ta intanet

March 6, 2023

Hukumomin kasar Jamus sun sanar da gano wani gungun masu kutse ta intanet da ke da alaka da kasar Rasha.

https://p.dw.com/p/4OKKo
Symbolbild IT-Systeme
Hoto: Jochen Tack/IMAGO

Ana zargin gungun mai sunaye biyu "Indrik Spider" da "Doppel Spider" da yi wa sama da ma'aikatu 600 kutse wadanda galibinsu suke a Turai da kuma kasar Indiya, kuma an yi nasarar gano gungun ne da ban hannun hukumar binkicen ta kasar Amurka FBI da kuma 'yan sandan kasashen Holland da Ukraine. 

A cewar shugaban rundunar 'yan sandan Jamus mai bincike kan satar bayanai ta hanyar intanet Markus Hartman, bankado gungun na nuni da yadda barazanar satar bayanai ta hanyar itanet ke kera girma a kasashen duniya.

Tuni dai aka ba da sammancin wasu mutane uku makusantan fadar Kremlin da ake zargi da jagorantar gungun masu kutsen.

Dama dai Jamus ta yi ta fuskantar kutse daga Rasha ciki har da wanda aka yi a shekarar 2015 wanda ya dagula harkokin majalisar dokokin kasar da kuma wasu ofisoshi na fadar gwamnati a lokacin mulkin Agela Merkel.