1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta ja hankalin Koriya ta Arewa

November 8, 2017

Hukumomi a Jamus sun yi kira ga Koriya ta arewa da ta mika wuya ga tayin sulhu da Amirka ta yi dangane da gwajen-gwajen makamai, batun dake ci gaba da tayar da hankalin kasashe.

https://p.dw.com/p/2nHEW
Südkorea Raketentest
Hoto: picture-alliance/NurPhoto/South Korea Defense Ministry

Gwamnatin Jamus ta yi kira ga Koriya ta arewa da ta mika wuya ga tayin sulhu da Amirka ta yi dangane da gwajen-gwajen makaman nukiliya da masu linzami, batun dake ci gaba da tayar da hankalin kasashe musamman ma Amirka.

Kiran na gwamnatin Jamus, na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan wani gargadin da shugaba Donald Trump ya yi kan girman barazanar da Koriya ta arewa ke yi wa Amirkar da sauran kasashen duniya. 

Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamus, ya bayyana rashin tabbas kan manufofin Amirka karkashin jagorancin shugaba Donald Trump. Manufofin Amirkar a cewar mahukuntan na Jamus sun hada ne da bangaren cinikayya da kuma amfani da wasu kalamai kan Koriya ta arewa, musamman cikin 'yan kwanakin da ake ciki.