1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta fice daga rundunar Sophia

Gazali Abdou Tasawa
January 23, 2019

Bayan da Jamus ta sanar da shirin janye jiragen ruwanta daga rundunar yaki da fataucin bakin haure ta Turai ta Sophia, ta ce za ta ci gaba da halartar taron rundunar a hedikwatarta da ke a birnin Roma na Italiya.

https://p.dw.com/p/3C2Nf
Fregatte "Augsburg" läuft zur Operation "Sophia" aus NEU
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Assanimoghaddam

Jamus za ta ci gaba da kasancewa a cikin Rundunar hadin gwiwa ta sojin ruwan kasashen Turai ta Sophia da ke aikin yaki da masu fataucin bakin haure a gabar ruwan Libiya wannan kuwa duk da matakin da Jamus din ta dauka na janye jiragen ruwanta masu taimaka wa rundunar ta Sophia aikin sintiri a saman teku. A jiya talata ne dai rundunar sojin kasar ta Jamus ta sanar da wannan mataki nata.

Sai dai wata majiya mai tushe daga kungiyar ta EU  wacce ita ce ta kwarmata wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP wannan labari a wannan Laraba, ta ce akwai yiwuwar kasar ta Jamus ta sake aiko da wata rundunar sojin ruwan a cikin aikin yaki da masu fataucin bakin hauren ta teku a nan gaba kana Jamus din za ta ci gaba da halartar taron rundunar ta Sophia da ke da hedikwata a birnin Roma na Italiya. 

A ranar shida ga watan Febuwaru ne dai sojojin kasar ta Jamus na rundunar ta Sophie wadanda ke girke a birnin Augsburg za su soma aikin janye kayansu daga rundunar ta Sophia. 

A shekara ta 2015 ne kasashen Turai suka kafa rundunar ta Sophia domin yaki da masu fataucin bakin haure zuwa Turai ta teku. Kuma tun bayan kafata ta yi nasarar ceto bakin haure masu yawa a teku da kuma bayar da horo ga sojin ruwan kasar Libiya.