1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta yaba da zaben Burkina Faso

Suleiman BabayoDecember 2, 2015

Jamus ta shiga cikin kasashe da suka nuna gamsuwa da zaben kasar Burkina Faso da Christian Kaboré ya lashe.

https://p.dw.com/p/1HG4x
Burkina Faso Präsidentschaftswahl - Gewinner Roch Kaboré
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Ministan harkokin wajen kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi maraba da zaben da ya gudana na kasar Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka. Gwamnatin kasar ta Jamus ta nuna farin ciki da yadda zaben na karshe mako ya wakana cikin gaskiya da adalci tare da yaba wa shugaban gwamnatin wucin gadi Michel Kafando.

Hukumar zaben kasar ta ayyana Roch Marc Christian Kaboré tsohon firamnista a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da kashi 53 cikin 100, yayin da Zephirin Diabre yake matsayi na biyu da kashi 30 cikin 100, kuma tuni ya rungumi kaddara. Wannan zaben ke mayar da kasar ta Burkina Faso bisa tafarklin demokaradiyya bayan boren da ya kawo karshen gwamnatin Blaise Compaore ta shekaru 27 cikin shekarar da ta gabata.

Tuni zabebben shugaban kasar ta Burkina Faso Christian Kabore ya ce gwamnatinsa za ta saka himma wajen bunkasa tattalin arziki da samar da muhimman abubuwa na bakatun yau da kullum.