1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta yi na'am da shawarar Macron kan EU

Aliyu Abdullahi Imam
March 5, 2019

Gwamnatin Jamus ta jaddada goyon bayanta ga shawarar da shugaban Faransa Macron ya bayar kan yi wa kungiyar tarayyar turai kwaskwarima

https://p.dw.com/p/3EV7J
Weltmacron
Hoto: DW/B. Zemke

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi kiran yin gyaran fuska ga gudanarwar Kungiyar Tarayyar Turai, a kan matsalolin da ka iya tasowa sanadiyar masu nuna tsantsar kishin kasa a Turai. Kiran nasa na zuwa ne kimanin watanni uku a gudanar da zaben 'yan majalisun dokokin Tarayyar Turai. Ya yi nuni da cewa, ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai a ranar 29 ga watan Maris, na nuni da irin kalubalen da Tarayyar Turai ke fuskanta.

Gwamnatin Jamus, ta bakin mataimakin shugabar gwamnatin Jamus kuma ministan kudi Olaf Scholz, yace gwamnatin Jamus na goyon bayan shawarar ta Macron.