1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi wa 'yan gudun hijira sama da miliyan rijista a Jamus

Kamaluddeen SaniJanuary 6, 2016

Gwamnatin Jamus ta bayyana cewar akalla mutane miliyan daya da dubu dari daya ne aka yi musu rijista a matsayin masu neman mafaka a kasar a shekara ta 2015.

https://p.dw.com/p/1HZEo
Deutschland Innenminister Thomas de Maizière
Hoto: Getty Images/T. Lohnes

Ministan harkokin cikin gidan Jamus ya kara da cewar sama da 'yan gudun hijira dubu dari hudu ne suka futo daga kasar Siriya da ke kasancewa mafiya yawa.

Ministan harkokin cikin gidan na Jamus Thomas De Maiziere ya fada a ranar Larabar nan cewar kimanin mutane miliyan daya da dubu 91 ne aka yi musu rijista.

A inda ya kara da cewar 'yan Siriya su ne suke da tarin yawa da suka haura dubu 400 yayin da 'yan Afganistan ke da sama da dubu 154 masu biye musu baya su ne 'yan Iraki da suka yi kimamin dubu 122.

Jamus dai a karon farko na kasancewa kasa a tarayyar Turai da ta fi kowace kasa karbar 'yan gudun hijira masu yawa a shekara ta 2015.