1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta rubanya miloyoyin Euro ga Afirka

Abdul-raheem Hassan
December 4, 2017

Asusun kula da tallafin kasashen Afirka na Majalisar Dinkin Duniya ce za ta isar da kudaden, da zimmar inganta harkokin zabe da shari'a gabannin babban zaben da Somaliyan za ta gudanar a shekarun 2020 zuwa 2021.

https://p.dw.com/p/2okje
Somalia Mogadischu | wachsende Stadt
Hoto: DW/S. Petersmann

Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta ce za ta rubanya kudaden tallafinta ga kasar Somaliya nan da karshen wannan shekara. A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta sanya wa hannu, ta ce Somaliya za ta samu karin kudaden da za su kai Euro miliyan 3,25 kamin karshen wannan wata.

Ana sa ran Jamus za ta ba da wadannan makudan kudade ne ta asusun kula da tallafin kasashen Afirka na Majalisar Dinkin Duniya, da zimmar inganta harkokin zabe da shari'a gabannin babban zaben da Somaliyan za ta gudanar shekarun 2020 zuwa 2021.

Sauran fannoni da za a sarrafa wadannan kudaden dai sun hada da sha'anin tsaro da karfafa tsaro a fadin kasar, Somaliya dai na a cikin kasashen gabashin Afirka da ke fuskantar barazanar tsaro daga kungiyoyi irin su al-Shbaab kazalika kasar na fama da rashin abinci sakamakon fari da ya addabeta.